<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>253</hymn_number>
<title>Ya Allahna, Ƙarfafa ni LW253</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Allahna, ƙarfafa ni
 Loton da duniya ta cuɗe,
 Domin kullum in yabe ka, in yi nufinka

[V2]
 2) Ka buɗe mini idanu,
 In ga kasawar ƴan Adam,
 Idonka zai yi nasara, in yi nufinka.

[V3]
 3) Da hamdala da dangana,
 Da ƴanci zan yi sujada,
 Kullum in yi ta addu'a, in yi nufinka.

[V4]
 4) Ko'ina cikin ƃacin rai
 Zan sa dangana gare ka,
 Hikimarka ta bishe ni, in yi nufinka.

[V5]
 5) Da ikonka mai taimako,
 Zan kiyaye wa'adina,
 In manta da kaina, sai kai, in yi nufinka.

[V6]
 6) Algaitar Sama ta furta.
 Su gaskatawa, da bege,
 Da ƙauna sun yi nasara, in yi nufinka.</lyrics>
</song>